IQNA

Jam'iyyar Al-Wefaq Bahrain ta yi kira da a kawo karshen yaki kan kasar Yemen cikin gaggawa

22:19 - January 22, 2022
Lambar Labari: 3486853
Tehran (IQNA) Jam'iyyar Al-Wefaq ta Bahrain ta yi kira da a kawo karshen yaki da kuma kashe fararen hular Yemen wadand ba su da kariya.

Jam'iyyar National Jamiat al-Wefaq al-Islam a Bahrain ta yi kira da a tsagaita bude wuta a kan kasar Yemen da kuma aiwatar da gagarumin tsarin siyasa don kiyaye 'yancin rayuwa da 'yancin kasar Yemen.

Al-Wefaq ta jaddada cewa zabin yaki yana da barna, kuma kashe fararen hula da kai hare-hare ta sama a wasu sassa na kasar Yemen a cikin 'yan kwanakin nan, zai haifar da karin barna da rikici.

Al-Wefaq ta kuma jajantawa al'ummar kasar Yemen dangane da kisan da aka yi wa dimbin fararen hula a rana guda, lamarin da ke nuni da tabarbarewar harkokin jin kai a kasar.

Sama da mutane 90 ne da suka hada da kananan yara uku ne aka kashe a harin da jiragen yakin kawancen Saudiyya suka kai a Yammacin  ranar Juma’a 21 ga watan Janairu 2022, a cewar kungiyar Save the Children.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa ita ma ta tabbatar da cewa sama da mutane 100 ne suka mutu ko kuma suka jikkata sakamakon harin da kawancen Saudiyya ya kai a wani gidan yari da ke Saada da ke arewacin kasar Yemen a jiya.

Harin da sojojin kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai kan gidan yarin na Saada ya haifar da tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniya, daga ciki har da majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai.

4030361

 

captcha