IQNA

Ana Sake Gyaran Ginin Wata Coci Mai Shekaru 1600 A Yankin Zirin Gaza Palastinu

19:21 - January 25, 2022
Lambar Labari: 3486866
Tehran (IQNA) Jami'ai a zirin Gaza sun sanar da farfado da kuma maido da wani coci mai shekaru 1,600 a zirin Gaza da kuma bude shi ga maziyarta.

Ma'aikatar yawon bude ido da kayayyakin tarihi ta Falasdinu a zirin Gaza a yau 25 ga watan Janairu  ta bude coci mai shekaru sama da 1600 ga masu ziyara.

Majami'ar dai tana a garin Jabalya da ke arewacin zirin Gaza, kuma tana daya daga cikin muhimman wuraren tarihi na zirin Gaza, kuma a dunkule, daya daga cikin fitattun wurare a yankin Levant, a cewar Ibrahim Jaber, mataimakin ministan harkokin Yawon bude da kayan tarihi.

Jaber ya ce "Ma'aikatar ta yi nasarar sake gina majami'ar domin ta kara samun karbuwa ga masu ziyara da kuma zama abin tarihi na al'adu da tarihi ga al'ummar Palasdinu," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Wannan majami'a na daya daga cikin muhimman abubuwan tarihi na gabas ta tsakiya, domin ya hada da kayayyakin tarihi da majami'u da dama a yankin ba su da su."

Garin Gaza dai na daya daga cikin tsofaffin garuruwa a duniya, kuma ya kasance karkashin mulkin Fir'auna da sarki Giriki da Romawa kafin zuwan muslunci.

A cewar majiyoyin tarihi, daular Romawa ta mayar da haikalin maguzawa da gwamnatin Romawa ta gina a Gaza zuwa majami'u.

 

4031264

 

 

captcha