IQNA

Dan Takarar shugabancin Faransa Mai Tsananin Kiyayya Da Musulunci

22:55 - January 25, 2022
Lambar Labari: 3486868
Tehran (IQNA) Eric Zemour, dan takarar shugaban kasar Faransa mai ra'ayin rikau, ya bayyana shirinsa na sanya takunkumi kan Musulunci da alamomin Musulmi idan ya yi nasara.

Tashar aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Zemour ya wallafa bayanin ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa: Za a haramta sanya duk wani tufafi da ke dauke da alamomin Musulunci - ciki har da hijabi a wuraren da jama'a ke taruwa.

Bugu da kari, ya yi alkawarin haramta ayyukan kungiyoyin Musulunci, kamar kungiyar 'yan uwa musulmi, idan ya yi nasara.

A baya Zemour ya bayyana a wata hira da tashar talabijin ta France 2 cewa: "Idan ya zama shugaban kasa, zai hana Musulman Faransa sakawa 'ya'yansu sunan Muhammad."

Ya jaddada a cikin hirar cewa dokar za ta sanya kaidi kan sunayen da ake radawa yaran musulmi.

Wasu masu fafutuka musulmi sun jaddada cewa idan Eric Zemour ya lashe zaben shugaban kasa, da dama daga cikin  al'ummar musulmi da Larabawa a Faransa za su fice daga kasar.

 

https://iqna.ir/fa/news/4031402

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Tashar bayyana takunkumi wallafa
captcha