IQNA

Rahoton Isra'ila: Hezbollah za ta ci gaba da kasancewa mai tasiri a Lebanon

19:05 - January 26, 2022
Lambar Labari: 3486870
Tehran (IQNA) A cikin rahotonta na shekara, cibiyar nazarin harkokin tsaron cikin gida ta Isra’ila ta yi ishara da matsayi da tasiri na kungiyar Hizbullah a Labanon inda ta bayyana cewa Hizbullah za ta ci gaba da rike wannan matsayi.

Cibiyar yahudawan sahyoniyan a cikin wani rahoto mai suna "dabarun Isra'ila na 2022 " wanda ake shirya domin yin bita kan manyan kalubale da gwamnatin Isra’ila za ta iya fuskanta a shekara, ya bayyana matsayin Hizbullah da tasirinta a Lebanon a matsayin daya daga cikin manyan kalubale na wannan shekara.

Baya ga sanya Iran, Iraki, Siriya, Labanon, Palastinu, da Yemen a matsayin kalubalen tsaro ga gwamnatin yahudawan Isra’ila, rahoton ya kuma rubuta game da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma irin karfin da wannan yunkuri take da shi a matsayin babbar barzana ga samuwar Isra’ila.

Rahoton ya ce saboda tasirin kungiyar ne da kuma matsayinta a Labanon, wasu a kasar ke kiran sunan gwamnatin Lebanon da aka kafa a watan Satumban da ya gabata, da sunan gwamnatin Hezbollah, saboda said a kungiyar ta akince ne sannan aka iya kafa gwamnatia  kasar.

Rahoton na wannan cibiya ta yahudawan sahyoniya ya kara da cewa: a fili yake cewa akwai matsin lamba kan kungiyar Hizbullah a mataki na kasa da kasa, amma kuma hakan ba zai iya rage karfinta ko tasirinta a kasar Lebanon ba.

Rahoton tsare-tsare na gwamnatin sahyoniyawan ya kammala da cewa, Hizbullah za ta ci gaba da ci gaba da samun karuwar tasirin da take da shi a kasar Labanon ta fuskar siyasa da soja da tattalin arziki da zamantakewa duk kuwa da matsin lamba na ciki da waje a kanta.

 

4031636

 

 

captcha