IQNA

An Tarjama Kur'ani Mai Tsarki A Cikin Harshen Girkanci A Masar

19:57 - January 26, 2022
Lambar Labari: 3486871
Tehran (IQNA) Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da zaɓen tarjamar kur'ani mai tsarki zuwa harshen Girka a ƙarƙashin kulawar ma'aikatar.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar Mohamed Mukhtar Juma ya sanar a shafinsa na Twitter cewa ma'aikatar ta buga zaben tarjamar  kur'ani mai tsarki da harshen Greek.

 Mukhtar Juma ya kara da cewa a shafinsa na Tuwita, an gudanar da wannan tarjamar ne bisa kokarin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar, musamman ma tafsirin Kalmar Allah da kuma buga imomin kur’ani mai tsarki.

Tun da farko, ministan harkokin addini na Masar ya amince da tarjamar kur'ani mai tsarki zuwa harshen Urdu, da Ahmad Mohammed Ahmad Abdul Rahman, malami a tsangayar harsuna da tarjama a jami'ar Al-Azhar, ya amince da shi, wanda ya gabatar da jawabi a taron.

 

4031516

 

captcha