IQNA

Fitaccen Malami Masanain Tafsisrin Kur'ani Bafalastine Ya Rasu

19:56 - January 29, 2022
Lambar Labari: 3486879
Tehran (IQNA) Sheikh Salah Abdel Fattah al-Khalidi, daya daga cikin manyan malaman Falasdinawa a fagen tafsiri da ilimin kur’ani mai tsarki, ya rasu a jiya yana da shekaru 74 a duniya.

Sheikh Salah Abdul Fattah al-Khalidi, masanin ilimin tafsiri da ilimin kur’ani mai tsarki ya rasu sakamakon ciwon zuciya da ya yi fama da shi.

An haifi Al-Khalidi mai shekaru 74 kwararre kan tafsirin kur’ani mai tsarki a birnin Jenin na Falasdinu, inda daga bisani ya koma kasar Jordan tare da iyalansa.

Mawallafin Bafalasdine ya sami gurbin karatu a shekarar 1965 a Al-Azhar, sannan ya shiga tsangayar shari'a  wato Faculty of Sharia, kuma ya kammala a shekarar 1970.

A shekarar 1977, ya sami digirinsa na biyu a jami'ar Imam Muhammad bin Saud da ke Riyadh, inda ya yi rubutun kammala karatun nasa a wannan bangare mai taken “Sayyid Qutb da siffar fasaha a cikin Alkur’ani.

Salah Abdel Fattah ya sami digirinsa na uku a fannin Tafsirin Alqur'ani da Kimiyya a Jami'ar Imam Muhammad Ibn Saud a shekarar 1984.

Bayan kammala karatunsa na Al-Azhar ya zama jami'i Ma'aikatar shari'a ta kasar Jordan a birnin Tufilah, kuma a shekara ta 1974 ya zama mai kula da harkokin addini na ma'aikatar.

درگذشت اندیشمند فلسطینی حوزه تفسیر و علوم قرآنی

 

https://iqna.ir/fa/news/4032040

Abubuwan Da Ya Shafa: bafalastine
captcha