IQNA

Za a gudanar da taron kasa da kasa na matasa kan nazarin rayuwar manzon Allah (SAW)

20:14 - January 29, 2022
Lambar Labari: 3486880
Tehran (IQNA) taron kasa da kasa mai taken darussa daga rayuwar"Manzon Allah (SAW) ga matasa wanda zai gudana a karkashin tsangayar ilimin tauhidi da ilimin addinin musulunci na jami'ar Tehran.

Wannan taro zai gudana ne ta hanyar yanar gizon yana gudana ne daidai da jerin shirye-shiryen kasa da kasa a tsangayar ilimin tauhidi da ilimin addinin musulunci na jami'ar Tehran, wanda kuma shi ne karo na farko da za a gudanar ta hanyar gizo.

A yau ne za a fara gudanar da wannan taro  29 ga watan Janairu daga karfe 3 zuwa 6 na yamma tare da hadin gwiwar mataimakin cibiyar nazarin al'adu na juyin juya halin Musulunci na kasa da kasa kuma za a gudanar da shi cikin harsunan Ingilishi da Larabci.

Masana da malaman jami'a daga kasashen Iraki, Malaysia, Kanada, Amurka, Indiya, Burtaniya da Serbia na daga cikin mahalarta taron, kamar yadda kuma za su gabatar da jawabai a taron.

za a iya shiga taron kai tsaye ta hanyar adireshin yanar gizo kamar haka:

https://www.skyroom.online/ch/csir.ut/ ut »an gudanar

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4032088

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kai tsaye Burtaniya
captcha