IQNA

21:34 - February 05, 2022
Lambar Labari: 3486911
Tehran (IQNA) An yi wa ministan harkokin addini na kasar Tunisiya bayani kan yadda aka buga cikakken kur'ani mai tsarki na farko na makafi.

Ministan harkokin addini na kasar Tunisiya Ibrahim Al-Shaybi ya ziyarci cibiyar buga kur'ani mai tsarki ta Jami'at Absar a jiya, Alhamis 4 ga watan Fabrairu, a ci gaba da buga kur'ani mai tsarki da haruffan makafi wanda ake yi a karon farko a kasar.

Al-Shaybi ya ce za a ba da kur’ani kyauta ga cibiyoyi da daidaikun mutane da ke bukatar taimakon makafi don karanta kur’ani mai tsarki.

Ya ba wa babban darakta na cibiyar kula da harkokin kur’ani izinin kammala buga dukkan sassan kur’ani mai tsarki.

A baya ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunusiya ta sanar da cewa, domin gudanar da hidimar kur’ani mai tsarki da kuma saukaka wa makafi karanta Kalmar Allah, ta buga kashi na 30 na kur’ani mai tsarki wanda Qalun ya rawaito a cikin haruffan Braille.

Kungiyar Absar ce ta buga wannan bangare na kur'ani mai tsarki tare da izinin kwamitin musulmi na majalisar koli ta Musulunci ta kasar Tunisia, bayan da malamai suka yi nazari a kai.

 

https://iqna.ir/fa/news/4033672

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: