
Jeremy Corbyn, tsohon shugaban jam'iyyar Labour ta Biritaniya, ya yi kira da a tuhumi Isra'ila kan zalunci da cin zarafi da take yiwa Falasdinawa.
A shafinsa na Twitter, Jeremy Corbyn ya yi kira ga kasashen duniya musamman Amurka da Tarayyar Turai da su yi kokarin kawo karshen wariya da samar da zaman lafiya a yankin cikin adalci da mutuntawa, tare da tabbatar da daidaiton hakkin dan Adam.
Corbyn ya ce "Dole ne shugabannin duniya su dauki matakin gaggawa don hukunta gwamnatin Isra'ila da kuma dorawa gwamnatin Isra'ila alhakin musgunawa Falasdinawa."
"Abin da ke faruwa ga Falasdinawan dabbanci ne kuma laifi ne na cin zarafin bil'adama," in ji shi, yayin da yake mayar da martani ga rahoton Amnesty International kan wariyar da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a wani rahoto da ta fitar a ranar Talatar da ta gabata, ta ce kamata ya yi a hukunta jami'an Isra'ila kan laifukan wariyar da suke nuna wa Falasdinawa.
DYa ce duk kuwa da adawar da Isra'ila ke yi da wannan rahoto, Muna kira ga hukumomin Isra'ila da su gurfanar da wadanda ke da hannu wajen cin zarafin bil'adama.
https://iqna.ir/fa/news/4034196