IQNA

Gwamnatin Syria Ta Yi Maraba Da Jingine Batun Bai Wa Is’ila Kujerar Mamba A Tarayyar Afirka

21:13 - February 08, 2022
Lambar Labari: 3486926
Tehran (IQNA) Kasar Siriya ta yi maraba da matakin da kungiyar Tarayyar Afirka ta dauka na dakatar da batun baiwa gwamnatin Isra’ila kujera a matsayin mai sa ido a wannan kungiya.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Wata majiya a hukumance a ma'aikatar harkokin wajen Syria ta shaidawa SANA cewa, matakin dakatar da kasancewar Isra'ila a cikin kungiyar Tarayyar Afirka, wani tabbaci ne na nuna goyon bayan kungiyar ga Falasdinu.

Ya kara da cewa: Wannan matakin na nuni da yadda wannan gwamnatin ta 'yan ta'adda ta ke kara zama saniyar ware da kuma yin Allah wadai da munanan manufofinta na nuna wariya, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.

A ranar Lahadin da ta gabata ce kungiyar Tarayyar Afirka baki daya ta dakatar da lasisin Isra'ila a matsayin mamba a kungiyar, kuma an kafa kwamitin da ya kunshi shugabanni bakwai da suka hada da shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Teboun domin duba lamarin.

Bayan wannan shawarar, kungiyar hadin kan Larabawa da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu Hamas su ma sun yi maraba da shi.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne aka ba wa gwamnatin sahyoniyawan izinin zama mamba a kungiyar Tarayyar Afirka a hukumance, kuma jakadiyar Isra'ila a kasar Habasha Allie Edmaso ta mika wa Musa Faqi Muhammad shugaban hukumar Tarayyar Afirka takardar shaidar zama mai sa ido ga kungiyar Tarayyar Afirka.

4034798

 

4034798

captcha