Bassem Naeem, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a zirin Gaza, ya ce duk wani keta jan layi a unguwar Sheikh Jarrah ko masallacin Al-Aqsa, ko kuma a dukkanin wurare a birnin Kudus, zai haifar da mummunan sakamako, kuma zai iya haifar da wani sabon rikici.
Ya kara da cewa Kudus ita ce alkiblar musumi ta farko kuma wani bangare ne na akidar al'ummar musulmi kuma abin da ke faruwa a cikinta ba wai kawai yana da alaka da al'ummar Kudus ba har ma da batun Palastinawa da Larabawa da musulmi.
A jiya ne dai Isra'ila ta kai farmaki kan Falasdinawa da dama a unguwar Sheikh Jarrah da ke gabashin birnin Kudus tare da kafa shingaye.
Ya ce kungiyar Hamas na sa ido sosai kan halin da fursunonin Falasdinawan da ke gidajen yarin Isra'ila ke ciki tare da dagewa a kan wajabcin samar musu da dukkanin kayayyakin more rayuwa.
Fiye da fursunonin Falasdinawa 4,500 ne ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar alkalumman baya-bayan nan da aka fitar a watan Janairun da ya gabata.
https://iqna.ir/fa/news/4037127