IQNA

Hubbaren Imam Musa Kazem (AS)

Tehran (IQNA) An haifi Imam Musa Ibn Ja'afar (AS) wanda aka fi sani da Imam Musa Kazem (AS), limami na bakwai a cikin ahlul bait (AS) a ranar ashirin ga watan Zu al-Hijjah shekara ta 128 bayan hijira.

Imam Musa Ibn Ja'afar (AS) wanda aka fi sani da Imam Musa Kazem (AS), limami na bakwai a cikin ahlul bait (AS)  an hife shi ne a ranar ashirin ga watan Zu al-Hijjah shekara ta 128 bayan hijira, a kauyen Abuwa (a tsakanin Makkah da Madina).
Imam Kazim (AS) wanda halifofin Abbasiyawa musamman Haruna Rasheed suka tsananta masa, ya kasance a gidan yari na tsawon shekaru da dama a gidajen yari daban-daban na wadannan azzaluman mahukunta.
Daga karshe bayan shafe shekaru a gidan yari an shayar da shi guba ya kuma yi shahada a gidan yarin Bagadaza a ranar 25 ga watan Rajab shekara ta 183 bayan hijira.