IQNA

Ashtia:Gwamnatin yahudawa na Magana kan yakin Ukraine alhali tana kashe Falastinawa

18:22 - March 07, 2022
Lambar Labari: 3487021
Tehran (IQNA) A yayin da yake mayar da martani kan shahadar wani matashin Bafalasdine da yahudawa suka harbe a gabashin birnin Kudus, Firaministan Palasdinawa ya ce Isra'ila na amfani da batun yakin Ukraine saboda dalilain siyasa alhali tana kashe Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya nakalto Muhammad Ashtia firaministan hukumar Falasdinu yana cewa gwamnatin sahyoniyawan tana cin zarafin Falasdinawa, a daidai lokacin da take batun yakin Ukraine da neman shiga tsakanin bangarorin yakin.

Ya mayar da martani game da shahadar wani matashin Bafalasdine sakamakon harbin da mayakan yahudawan sahyoniya suka yi a garin Abu Dhais da ke gabashin birnin Kudus a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin Falasdinu Ibrahim Malhem ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Ashtia ya yi gargadi kan illar da ke tattare da karuwar kashe-kashe da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a yankunan da ta mamaye da kuma babatun da take yin a cewa ana cin zarafin muatne a yakin Ukraine.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a yammacin Lahadin da ta gabata shahadar wani matashin Bafalasdine a gabashin birnin Kudus.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce, Yaman Nafiz Jafal matashin Bafalasdine mai shekaru 16 da haihuwa ya yi shahada a hannun dakarun yahudawan sahyuniya a garin Abu Dhais da ke gabashin birnin Kudus.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya nakalto daga majiyar kasar ta na cewa yahudawan sahyuniya sun bindige shi ne sannan daga bisani suka jefa shi cikin motar soji.

 A watan Janairun da ya gabata, an ba da wasu sabbin umarni ga sojojin Isra'ila, kan cewa za su iya harbin Falasdinawa da ke jefarsu da duwatsu, ko da bayan matasan Palasdinawa sun gudu.

A safiyar Lahadin da ta gabata ne wani Bafalasdine dan shekaru 19 mai suna "Karim al-Qawasemi" ya yi shahada a hannun yahudawan sahyuniya a tsakiyar birnin Kudus da ke mamaye bisa zarginsa da raunata wasu sahyoniyawan biyu.

4041033

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawan sahyuniya
captcha