IQNA

Tunisiya Ta Bukaci Daukar Mataki Kan Laifukan Yakin Isra'ila

19:11 - March 23, 2022
Lambar Labari: 3487083
Tehran (IQNA) Ministan harkokin wajen kasar Tunusiya ya bukaci kasashen musulmi da su hada kai wajen kawo karshen laifukan yahudawan sahyoniya da take hakkin Falasdinu a kullum.

Ministan harkokin wajen kasar Tunusiya ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar hadin kan kasashen musulmi da su dauki nauyin al'ummar Palastinu da kuma kawo karshen take hakkin Falasdinawan da Isra'ila ke yi a kullum, da hare-haren da ake kai wa wurare masu tsarki da kuma manufofin Isra’ila na mamamye Falastinu da gina matsugunnai.

A jawabinsa a taro karo na 48 na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar OIC da aka fara a Islamabad babban birnin kasar Pakistan, Osman al-Jarndi ya jaddada bukatar a hada kai wajen tinkarar kalubalen ci gaban kasa da kasa da kuma dakile tasirinsu ga tsaro da zaman lafiya, duniya baki daya, musamman yankunan Larabawa da na Musulunci.

Al-Jarandi ya kuma yi kira da a kara kaimi wajen yin amfani da hanyoyin kariya da kuma daukar kwararan matakai don dakile ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da kuma laifukan da suka shafi kasashen duniya, kamar shige da fice ba bisa ka'ida ba da safarar mutane.

Al-Jarandi ya kuma yi kira da a yi amfani da na’urorin sadarwa na zamani na zamani wajen magance jawaban nuna wariya, da kyamar Musulunci.

Ya jaddada bukatar kara karfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ci gaba tare da halartar dukkanin cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma cibiyoyi na musamman masu fafutuka a fannin tattalin arziki don tinkarar rikice-rikice, musamman kalubalen da annobar Corona ke haifarwa da illolinsa.

Abubuwan Da Ya Shafa: zaman lafiya hakkin Falasdinawa
captcha