Kamfanin dillancin labaran Palestin e ya bayar da rahoton cewa, da safiyar yau ne dai kungiyar ta gwagwarmayar musulunci Hamas ta sanar da shahadar mayakan uku inda ta bayyana cewa; Kashe Palsdinawa da HKI take yi ba zai taba sa mamayar da ta yi wa Palasdinu ta zama halartacciya ba.
Sojojin Sahayoniyar dai sun bude wuta akan samarin palasdinawan ne a yankin Janin, inda su ka barsu a kwance suna zubar jinni har su ka yi shahada.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta ce; Siyasar kisan gilla wacce makiyan suke amfani da ita akan al’ummarmu a yankunan yammacin kogin Jordan da birnin Kudus ba za ta ba su tsaro da zaman lafiya, balle kuma su sami halascin zama a Palasdinu.
Kungiyar Jihad Islami a yayin da take jajantawa shahadar mayakanta guda uku, ta jaddada cewa jihadi da gwagwarmayar al'ummar Palastinu na ci gaba da yakar 'yan mamaya.
Bayanin na kungiyar Jihadin Islama ya bayyana cewa makiya yahudawan sahyoniya sun sake aikata wani laifi a ranar farko ta watan Ramadan tare da shahadar mayakan Palastinawa 3.
Sanarwar ta ce matakin da Falasdinawa za su dauka kan wannan aika aika zai dace da abin da laifin da aka aikata.
Jihadul Islami ta dora alhakin dukkan sakamakon wannan aika-aika da gwamnatin sahyoniyawan ta yi, akan mahukunatn gwamnatin yahudawan, kuma jinin wadanda aka kashe ba zai tabi haka nan ba.
Yan gwagwarmayar uku da su ka yi shahadar dai su ne; Khalil Dhawalibah, Sa’ib Abahirah, sai kuma Saif Abu Labdah.