Tehran (IQNA) Da yammacin Juma'a ne wasu malamai da masana kwamitin Istihla na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei suka yi kokarin ganin jinjirin watan Ramadan a birnin Qum.
Ba su ga jinjirin watan ba, don haka ne ranar farko ta watan mai alfarma za ta fado a ranar Lahadi a nan Iran.
Istihlal yana nufin kokarin ganin jinjirin wata da ke tabbatar da farkon wata a kalandar Hijira.