Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya saboda fargabar fushin Palasdinawa a unguwar Bab al-Amoud da ke birnin Kudus a wannan yanki, ta ayyana matsayinta na yin shiri.
'Yan sandan gwamnatin mamaya sun jibge dakaru kusan 3000 tare da kayan aiki a tsohon yankin na birnin Quds.
Muryar Kudus ta kuma ruwaito cewa, sojojin mamaya sun yi luguden wuta da harsasai na robobi da bama-bamai kan matasan Falasdinawa a Bab al-Amoud a yammacin Lahadi.
Yankin Bab al-Amoud ya gamu da kazamin fada tsakanin yahudawan sahyoniya da al'ummar Kudus a cikin watan Ramadan na shekarar da ta gabata, sakamakon adawar gwamnatin yahudawa ta nuna na gudanar ayyukan ibada a cikin masallacin Quds, musamman sallar asham.
Sojojin gwamnatin mamaya sun kai farmaki kan gidajen Falasdinawa a cikin tsoffin unguwanni na birnin Kudus da aka mamaye a cikin 'yan kwanakin nan tare da kame wasu da dama daga cikinsu.
Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan mai ci Yair Lapid ya ziyarci yankin Bab al-Amoud a yammacin Lahadi, 3 ga watan Afrilu, a daidai lokacin da aka girke dakarun mamaya masu tarin yawa a wurin.