IQNA

An Karrama wadanda Suka Lashe Gasar Kur'ani Ta Kasar Qatar

22:50 - April 22, 2022
Lambar Labari: 3487202
Tehran (IQNA) A wani biki da ya samu halartar iyayen yara da matasa da suka halarci gasar haddar kur’ani mai tsarki a kasar Qatar, an karrama wadanda suka fi nuna kwazo.

A jiya (Alhamis) Gidauniyar Al'adu ta Qatar ta karrama yaran da suka shiga gasar kur'ani mai tsarki karo na 11.

A daya bangaren kuma iyayen wadanda suka halarci gasar  sun yi godiya tare da nuna jin dadinsu da yadda gasar ta kayatar da kuma gagarumin kokari da kungiyar al’adu ta yi na gudanar da wannan gasa ta musamman a cikin watan Ramadan karkashin kulawar gogaggun alƙalai.

Sheikh Mohammad Maki, mahaifin yara uku da suka halarci gasar, ya bayyana farin cikinsa da sake gudanar da gasar haddar kur’ani mai tsarki tare da halartar yara kanana bayan an rage matakan kariya daga kamuwa da cutar korona.

Abdullah Saadoun, mahaifin wani yaro, ya yaba da gagarumar rawar da cibiyar ke takawa tare da hadin gwiwar ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci.

Shi ma Ahmad Suleiman, mahaifin wani yaro da ya halarci gasar, ya bayyana farin cikinsa da yadda dansa ya samu nasarar zama na daya a gasar tare da kammala haddar suratu Ahzab, ya kuma bayyana muhimmancin karfafa gwiwar yara kan yin amfani da harshen larabci da ma’anarsa na Alkur'ani mai girma daidai.

Sinan Abdul Karim, mahaifin Faisal Abdul Karim, ya ce: "Wannan Gasar haddar Al-Qur'ani na daya daga cikin fitattun ayyukan da gidauniyar Katara ta gudanar a cikin watan Ramadan, karatun kur'ani, nazari da haddar kur'ani ya shiga cikin tabbataccen tsarin cibiyar.

Faisal Sinan daya daga cikin mahalarta taron ya bayyana farin cikin sa inda ya ce ya koyi abubuwa da dama ta hanyar shiga wannan gasa ta karatu da haddar Littafi Mai Tsarki.

 

https://iqna.ir/fa/news/4051696

captcha