IQNA

Bayar da tallafin kayan abinci ga mabukata a Najeriya

20:57 - April 26, 2022
Lambar Labari: 3487219
Tehran (IQNA) Masallacin kasa da ke Abuja a Najeriya ya bayar da tallafin abinci ga musulmi 200 mabukata.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wani jami’in masallaci kuma shugaban kungiyar agaji da ke da alhakin raba kayayyakin, Mohammad Kabir Adam, ya ce sun dauki wannan mataki ne don ciyar da al’ummar musulmin da ke bukatar abinci domin saukaka musu azumin watan Ramadan.

Adamu ya ce: “Wannan taimakon da ake yi wa mabukata ya samo asali ne daga nasihohin addini da ke jaddada bayar da sadaka a cikin watan Ramadan.

Ya ce wannan shiri shi ne shiri na farko da wannan masallacin ya aiwatar, inda ya ce wannan yunkuri na daga cikin ayyukan jin kai da masallacin ke yi na taimakon iyalai mabukata a fadin kasar.

Masallacin kasa na Abuja ko kuma National Mosque, an gina shi ne a shekarar 1984, kuma an san shi a matsayin daya daga cikin alamomin birnin Abuja da kuma cibiya ta addinin musulunci.

 

https://iqna.ir/fa/news/4052559

captcha