
Al-Amiri ya bayyana a cikin jawabin nasa a yayin gudanar da taron kasa da kasa karo na uku na tunawa da "Ranar Quds ta kasa da kasa", cewa dukkanin makirce-makircen da ake kullawa kan kasar Iraki suna bayan sahyoniyawan ne.
Ya kara da cewa: Ranar Kudus ta zama fata da Falasdinawa suke rayuwa a cikinta, kuma muna kokarin ganin an cimma ta, yana mai jaddada wajabcin mai da hankali kan Kudus, da kuma tababtar da cewa ba a kulla a hulda gwamnatin yahudawan Sahyuniya da kasashen musulmi da na larabawa ba, musamman kasar Iraki.
Al-Amiri ya yi nuni da cewa, ‘yan Majalisar dokokin kasar Iraki sun daga tutar ‘yantar da al’ummar Palastinu kafada da kafada, suna jaddada matsayarsu ta yin watso da duk wani makirci na hada kai da Isra’ila.