IQNA

Noman furanni a kudu maso yammacin Iran

MEYMAND (IQNA) – A karshen watan Mayu shi ne lokacin girbi na furen damask a duk fadin Iran. Manoma suna fara girbi da sassafe kuma su ci gaba da aikin kafin rana ta yi zafi sosai.

Sannan ana sarrafa furannin don samar da ruwan fure ko "Golab". Hotunan da ke gaba suna nuna yadda ake girbi a Meymand, lardin Fars.