IQNA

Shiri na zahiri don haddace suratu Yasin a Vienna

17:34 - May 15, 2022
Lambar Labari: 3487296
Tehran (IQNA) Cibiyar Musulunci ta Imam Ali (AS) da ke Vienna, babban birnin kasar Austria , ta aiwatar da wani shiri na haddar Suratul Yasin cikin makonni 24.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, an fara gudanar da wannan aiki mai taken “karatun kur’ani tare da ni” a birnin Vienna, kuma an fara aiwatar da shi a wani dandali na wayar da kan jama’a a tashar telegram na cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke Vienna a “https://t.me/ iznin".

A kowane bangare na wannan shiri ana dora ayoyin suratu Yasin a tashar Telegram na cibiyar Musulunci ta Vienna, kuma masu sauraron wannan cibiya da masoya wannan cibiya za su iya amfana da ita ta hanyar ziyartar wannan tasha.

Karatuttukan da aka ɗorawa suna da tsawon minti ɗaya kuma ana sanya su cikin makonni 24 da muryar "Hussein Isfahanian" daga mahardatan Iran, kuma kashi na farko ya ƙunshi aya ta 1 zuwa 6 na Yasin.

A jiya 15 ga watan Mayu a kashi na biyu na shirin an sanya aya ta 7 zuwa ta 9 a cikin suratul Yasin ga masu sha'awar haddar Alkur'ani a tashar Telegram na cibiyar Musulunci ta Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna, kuma wannan shirin. har yanzu yana gudana.

 
captcha