IQNA

17:55 - May 26, 2022
Lambar Labari: 3487346
Tehran (IQNA) Hukumar kula da kayayyakin halal a kasar Ghana ta yi gargadi game da yin amfani da alamar jabun halal kan kayayyaki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘Business Ghana’ cewa, wata sanarwa daga kwamitin tabbatar da halal na kasa (NHCC) ta shawarci jama’a da su rika duba takardar shaidar halal da hukumar ke bayarwa a koda yaushe tare da tabbatar da sa hannun kwamitin da hatimin kayayyakin.

Sanarwar ta ce wasu mutane na cin zarafi da tambarin kwamitin da kuma takardar shedar bayar da shaidar halal ga kamfanoni da ake kira Ofishin Jagoran Musulman Ghana.

Sanarwar ta kuma kara da cewa kungiyar Tijjaniyya (TMMG) ba ta bayar da wasu takardun shaida na shari'a da ya halatta in ban da wanda ofishin Jagoran Musulmin Ghana (ONCI) ya bayar da kan wasikar NHCC.

An kafa kwamitin tabbatar da Halal na kasa ne a shekarar 2017 a wani kokari na hadin gwiwa tsakanin ofishin shugaban musulman Ghana (ONCI) da kungiyar Tijjan Islami (TMMG).

Kwamitin yana duba kayayyaki da kamfanoni don tabbatar da cewa kayayyakinsu sun dace da tsarin Musulunci.

4059804

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: