IQNA

15:31 - May 27, 2022
Lambar Labari: 3487347
Tehran (IQNA) Hanyar Imam Sadiq (AS) wajen tafsirin Alkur'ani ta ginu ne a kan bincike da tunani da ijtihadi, ya kuma koyar da dalibansa yadda za su iya fitar da nazari da ilimi mai zurfi daga kur’ani wajen fassara bangarorinsa.

Imam Sadiq (AS) a tafsirin Alkur’ani ya ce ya yi amfani da hanyoyi daban-daban wadanda suka zama wajibi kuma suka dace a kowane bangare.

Ya yi shahada ne a ranar 25 ga watan Shawwal shekara ta 148 hijira kamariyya, shekara ta (765 miladiyya).

Daya daga cikin muhimman ayyukan Imam Sadiq (AS) shi ne yin bayani da tawili da bayyana hukunce-hukunce da ruwayoyi da ayoyin Alkur’ani.

Waɗannan ayyuka sun fara kuma sun ci gaba bisa hanyar kimiyya. Ya yi amfani da tsarin Kur'ani tare da Kur'ani wajen fassara Kur'ani.

A cikin misalin Alqur’ani da Alqur’ani, kowace aya ana yin nazari ne bisa wasu ayoyi, wadda aka fi sani da tafsirin Alqur’ani da Alqur’ani.

Wani daga cikin hanyoyin kuma shi ne tafsirin Alkur’ani bisa tarihin rayuwar Manzon Allah (SAW) da Ahlul-Baiti (AS), wanda aka yi nazari kan tarihin Imamai na ahlul bait da ruwayoyin da aka samo daga gare su.

Tafsirin Kur'ani ta hanyar lafazi  wata hanya ce ta bayanin Kur'ani. Ta wannan hanya ne aka yi la’akari da lafuzzan Kur’ani kuma aka fassara Alkur’ani a kan su.

Hanyar daidaitawa ita ce wata hanyar Imam Sadiq  (A.S) na tafsirin Alkur'ani; Wannan hanya tana nufin daidaita aya zuwa ga al'amura daban-daban, A haƙiƙa, wasu ra'ayoyin da suke cikin kur'ani dole ne su sami misalai a waje a cikin duniya, kamar koramu da nau’oin bishiyoyi ko tirrai ko abinci ko kayan marmari da makamantan haka da aka ambata a cikin kur’ani da sunayensu, wanda kuma Imam Sadiq  (AS) ya ba da misali da fassarar ayoyi ta wannan hanya.

A takaice, Hanyar Imam Sadiq (AS) wajen tafsirin Alkur'ani ta ginu ne a kan bincike da tunani da ijtihadi, da kuma ruwaya, ya kuma koyar da dalibansa yadda za su iya fitar da nazari da ilimi mai zurfi daga kur’ani wajen fassara bangarorinsa.

3975786

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: