Jami’an ‘yan sandan kasar Indiya sun kama jigo kuma shugaban ‘yan kishin addinin Hindu karkashin jagorancin firaminista Narendra Modi bisa zarginsa yada kalaman kyamar musulmi a shafukan sada zumunta.
Kalaman da wannan jigo a jam'iyya mai mulki a Indiya ya yi na cin mutuncin manzon Allah (SAW) ya haifar da matsaloli tsakanin gwamnatin Indiya da wasu kasashen musulmi.
Wani babban jami’in ‘yan sandan Indiya ya ce an kama dan siyasar Indiyan ne da laifin yin kalaman tunzura jama’a a kan musulmi, kuma an tsare akalla wasu 50 bayan tashin hankalin da ya barke a Kanpur.
Jawabin wasu jami'an jam'iyyar da ke mulkin kasar Indiya biyu na cin mutuncin Manzon Allah (SAW) a makon da ya gabata ya fuskanci martani mai zafi daga kasashen Qatar, Kuwait da Iran.