IQNA

Masallacin Massalikul Jinaan na Senegal Mafi Girma a Yammacin Afirka

Tehran (IQNA) – Masallacin Massalikul Jinaan (hanyoyin aljanna) wurin ibada ne na musulmi a Dhakar, babban birnin kasar Senegal.

Yana da kubbabai 9 da mintoci 5, tsayin su ya kai mita 78, kuma yana da karfin karbar masu ibada 10,000 a ciki da kuma 20,000 a farfajiyar sa, shi ne masallaci mafi girma a yammacin Afirka.

An bude Masallacin Massalikul Jinaan ne a shekarar 2019 bayan shafe shekaru 7 ana gina shi da kudi Euro miliyan 40.

 
Abubuwan Da Ya Shafa: Masallacin ، Massalikul Jinaan ، senegal ، musulmi ، afirka