IQNA

Sabbin hidimomi na masallacin Annabi a lokacin karatowar aikin Hajji

17:37 - June 11, 2022
Lambar Labari: 3487404
Tehran (IQNA) A jajibirin aikin Hajjin bana, masu kula da masallacin Annabi (SAW) sun shirya tsare-tsare don jin dadin mahajjatan dakin Allah da masallacin Annabi. Wadannan shirye-shirye sun hada da gyara kwafin kur’ani 155,000 a masallacin zuwa samar da aikace-aikace don saukaka al’amuran yau da kullum na alhazai da ma’aikata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, a jajibirin lokacin aikin hajji, masallacin ma’aiki ya maye gurbin wasu sabbin kwafi na kur’ani mai tsarki sama da 155,000 da wasu tsoffi, wadanda suka hada da kwafin kur’ani guda 9,357 da aka tarjamasu zuwa harsuna 52.

Abdul Rahman bin Abdul Aziz Al-Sadis, babban darekta na Masallacin Harami da Masjid al-Nabi, shi ma ya kaddamar da wani shiri na maraba da ayarin mahajjata majagaba a bana tare da taken " Hidimawa alhazanmu abin alfahari ne ga ma'aikatanmu." A wannan gangamin da ya kunshi tarbar maniyyata da masu ibadar masallacin Annabi, za a ba su kyaututtuka.

Har ila yau, Al-Sadis ya kaddamar da littafin "Labarin Masallacin Annabi: Tarihi da Figures". Bugu da kari, da nufin saukaka gudanar da aikin hajji a masallacin Annabi, an kaddamar da manhajar “Alhazai” karo na biyu da aka sabunta.

Wannan application yana da harsuna biyar a cikin iOS da harsuna bakwai a cikin Android domin saukaka mahajjata da masu ibadar Masallacin Annabi.

 

https://iqna.ir/fa/news/4063378

captcha