IQNA

​Dakarun Hashd Al-shaabi Bangaren Al’ummar Iraki Ne Ba Na Siyasa Ba

19:25 - June 13, 2022
Lambar Labari: 3487416
Tehran (IQNA) Babban kwamandan dakarun sa kai na al’ummar Iraki Hashd Al-shaabi (Popular Mobilization ) Faleh al-Fayyad, ya yi bayani kan mataki na gaba a kasar Iraki, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 8 da bayar da fatawar kafa dakarun.

Faleh al-Fayyad ya tabbatar da cewa, Hashd Al-shaabi za su ci gaba da rike tutarsu domin kammala abin da shahidai suka rubuta.

A yayin bikin cika shekaru 8 da kaddamar da fatawar jihadi da kuma kafa kungiyar Hashd Al-shaabi (Popular Mobilisation) Al-Fayyadh ya bayyana cewa, Hashd Al-shaabi a yau al'umma ce, kuma a yau ne ake bikin kaddamar da wadannan dakaru, wadanda suka yi sadaukarwa da rayuwarsu da kuma duk abin da suka mallaka domin kare kasarsu da al’ummarsu, da kuma kare karamar dan adam.

Al-Fayyadh ya yi nuni da cewa, Hashd Al-shaabi su ne fatattaki ‘yan ta’addan Daesha lokacin da suka kafa Daularsu a Mausil, da kuma wasu yankuna na Iraki da suka mamaye.

Haka nan kuma ya yi ishara da irin makirci da aka yi da kullawa tsakanin kasashen da suke nufin sharri ga Iraki domin rusa dakarun hashd, wadanda su en kashin bayan zaman lafiyar Iraki, tare da kawo karshen mamayar Daesh da ayyukan ta’addanci a kasar.

Sannan kuma ya yi ishara da yadda wadannan dakaru suka hada kan al’ummar Iraki wuri guda, yan sunnah da shi’a da Kurdawa da kiristoci da sauran bangarori na al’ummar kasar karkashin tutar hadin kai.

Babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Ayatollah Sayyid ali Sistani ne dai ya bayar da fatawar kafa rundunar sa kai ta al’ummar Iraki ta Hashd Al-shaabi, domin yaki da ‘yan ta’addan IS, wanda kuma su ne suka gama da su ‘yan shekaru bayan mamayar da Daesh ta yi wa wasu yankunan Iraki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4064002

 

captcha