IQNA

Rukunin Farko Na Alhazan Iran Sun kama Hanya

Tehran (IQNA) A safiyar yau Lahadi ne aka gudanar da wani biki a filin tashi da saukar jiragen sama na Imam Khumaini da ke birnin Tehran na jigilar alhazan Iraniyawa na farko da suka tashi zuwa kasar Saudiyya.

Jami’ai da dama da suka hada da Wakilin Jagora a Al’amuran Hajji da Aikin Hajji Hojat-ol-Islam Abdol Fattah Navab, Shugaban Hukumar Hajji da Alhazai Seyed Sadeq Hosseini da Ministan Hanya da Raya Birane Rostam Qassemi ne suka halarci bikin.