IQNA

Za a karrama  Abbas Khamehyar a kamfanin dillancin labaran Iqna

15:52 - June 21, 2022
Lambar Labari: 3487447
A gobe 22 ga watan Yuni ne  wannan kafar yada labarai ta IQNA za ta gudanar da bikin karrama Abbas Khamehyar tsohon mai ba da shawara kan al'adu na Iran a kasar Lebanon kuma mataimakin al'adu da zamantakewa na jami'ar Qum .

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, za a gudanar da wannan biki ne don karrama masana harkokin al’adu na kasa da kasa,tare da halartar masu fafutukar a bangaren  al’adu, a dakin taro na cibiyar kur'ani ta Shahid Taghavi.

Shirin mai taken "Zaman Lafiya" za a gudanar da shi ne a kasashen duniya domin kare yunƙurin da Abbas Khamehyar tsohon mai ba da shawara kan al'adu na Iran a Labanon ya yi.

Za a fara wannan biki ne da karanta sakon Mohammad Mehdi Ismaili, ministan al'adu da shiryarwar addinin muslunci na kasarmu, sai kuma Sheikh Naeem Qasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da Mohammad Wassam Al-Murtada ministan al'adu na kasar Lebanon. A cikin wani taron bidiyo, Hojjatoleslam da Muslim Hamid Shahriari, babban sakataren Islami online da Mohsen Hajimirzaei, tsohon ministan ilimi, Abuzar Ebrahimi Turkman, tsohon shugaban cibiyar  al'adun musulunci da sadarwa, za su yi magana da kai.

Abbas Khamehyar wani mutum ne da ya shahara a Iran da sauran kasashen duniya kuma ya yi ayyuka da dama wajen gabatar da Iran da juyin juya halin Musulunci a kasashen waje.

4065523

 

captcha