IQNA

Saudiyya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar farko ta watan Zul-Hijja

16:43 - June 30, 2022
Lambar Labari: 3487489
Tehran (IQNA) Saudiyya ta tabbatar da ganin jinjirin wata a kasar a jiya Laraba kuam yau alhamis ne 1 ga watan na Kasar Saudiyya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar farko ga watan Zu al-Hijja

A rahoton kamfanin dillancin labaran Sputnik Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Kasar saboda haka daga yau Alhamis ne lissafin watan zul-hijjah ke faraway.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci al’ummar musulmi daga sassa daban-daban na kasar da su duba jinjirin watan Zu al-Hijja da yammacin jiya Laraba 30 ga watan Dhiqaadah shekara ta 1443 bayan hijira.

A cikin bayanin da ta bayar a baya, Saudiyya ta bayyana cewa, duk wanda ya ga jinjirin watan da ido  to ya je ofishin kotun mafi kusa da shi ya rubuta rahotonsa na ganin jinjirin watan, ko kuma ya tuntubi reshe mafi kusa na kotun.

Saudiyya ta kuma kafa wasu kwamitoci da ke gayyatar duk masu sha'awar ganin jinjirin watan da su shiga cikin wadannan kwamitocin.

Saudiyya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar farko ga watan Zu al-Hijja bayan ganin jinjirin watana  ajiya.

4067613

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha