IQNA

Cibiyoyi 28 A Kuwait Sun Jaddada Rashin Amincewa Da Kulla alaka Da Gwamnatin Yahudawan Isra’ila

15:30 - July 18, 2022
Lambar Labari: 3487562
Tehran (IQNA) a cikin wata wasika da suka aike wa Sarkin kasar, cibiyoyi da kungiyoyi 28 na fararen hula a Kuwait, sun bayyana matukar adawarsu da duk wani mataki na kulla hulda tsakanin kasarsu da Isra’ila

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, wadannan cibiyoyi sun bayyana a cikin wannan wasikar cewa: ziyarar shugaban Amurka Joe Biden a yankin da kuma yadda ake ta hankoron sanya kasashen larabawa su kulla alaka da Isra’ila, muna sake jaddada matsayarmu ta dindindin kan kin amincewa da wannan lamarin bisa kowace irin hujja.

Har ila yau, wannan wasiƙar ta bayyana cewa: goyon bayan gwagwarmayar al'ummar Palastinu da kuma neman 'yancin dukkan yankunan da aka mamaye, buƙatu ne da suka cancanci dubawa domin kuwa kan ka’ida .

Wannan sanarwa ta samu sa hannun daukacin cibiyoyin guda 28 na kasar Kuwait, daga cikinsu akwai kungiyar lauyoyin Kasar, kungiyar masana zamantakewar al’umma, kungiyar injiniyoyin Kuwait da kungiyar kwadago ta kasar, da kuma kungiyar likitoci gami da Ƙungiyar Tsaron lafiyar Iyali ta Ƙasa da dai sauransu.

4071295

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kin amincewa goyon baya bukatu hujja wasika
captcha