IQNA

Al'ummar kasar Yemen sun gudanar da tarukan Eid Ghadir

15:59 - July 18, 2022
Lambar Labari: 3487563
Tehran (IQNA) Al'ummar kasar Yemen sun gudanar da bukukuwan idin Ghadir da gagarumin biki a birnin Sana'a da wasu larduna 13 inda suka gudanar da bukukuwa daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Manar cewa, al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani biki na tunawa da zuwan sallar Idin Ghadir tare da halartar dimbin jama’a da dama a dandalin Sana’a fadar gwamnatin kasar da kuma cibiyoyi na wasu larduna 13 na kasar Yemen.

Al'ummar kasar Yemen sun kuma rera takensu tare da yin Allah wadai da ziyarar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kai birnin Jeddah a baya-bayan nan da kuma kalamansa na nuna goyon baya ga gwamnatin sahyoniyawa da kuma kawancen cin zarafi na Saudiyya.

A wajen halartar wannan biki, al'ummar kasar Yemen sun bayyana soyayyarsu da sadaukarwarsu ga Sayyidina Ali (AS) da kuma tsarkin Ahlul-baiti tare da jaddada ci gaba da koyi da Ahlul Baiti (A.S) da sadaukarwa ga ma'aiki. sanadin gaskiya da fuskantar kafirai da makiya al'ummar musulmi.

Mahalarta wannan biki sun gudanar da wakokin yabo na Imam Ali (AS) da Ahlul Baiti. Yawancin wadannan wakokin sun samo asali ne daga sanannun al'adun mutanen Yemen.

An gudanar da wannan biki ne a Sana'a, babban birnin kasar Yemen, a yankuna uku da suka hada da dandalin Tahrir, da ke kusa da jami'ar Afsari da masallacin Jame al-Shaab, Haka kuma mata sun halarci irin wannan biki a yammacin yankin Al-Thura.

4071573

 

captcha