IQNA

Kungiyar Al-Azhar mai sanya ido kan kare hakkokin musulmi ta ce;

Wajibi ne a tsananta hukunci don kawo ƙarshen nuna wariya ga musulmi

15:39 - July 27, 2022
1
Lambar Labari: 3487599
Tehran (IQNA) A yayin da take yin Allah wadai da hare-haren wariyar da ake kai wa musulmi a Turai, kungiyar ta Al-Azhar Observatory ta jaddada wajibcin kara tsananta matakan hukunta wadanda suke aikata hakan, domin kawo karshen wariyar  da ake nuna ma musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar ta Al-Azhar Observatory da ke  yaki da tsattsauran ra'ayin kin jinin musulunci a duniya musammana  anahiyar turai, bayan harin da aka kai kan wata mata Musulma mai juna biyu a Italiya, ta yi gargadi kan karuwar wadannan hare-hare, saboda yaduwar kyamar musulunci daga bangaren masu tsattsauran ra'ayi.

A wannan harin, wani dan kasar Italiya mai shekaru 35 ya ci zarafin wata mata Musulma a lokacin da suka shiga jirgin kasa a gaban danta mai shekaru 11.

Mutumin dan kasar Italiya ya ci gaba da fadin kalaman wariya da cin zarafi a kan matar musulma.

Cibiyar sa ido ta Al-Azhar ta bayyana  cewa: bisa ga abin da 'yan sandan Italiya suka sanar, an kama wannan mutumi kuma yanzu haka yana fuskantar tuhuma da laifin kai hari da gangan da kuma cutar da wannan mata dad anta karami.

Haka nan kuma cibiyar ta yi ishara da karuwar irin wadannan ayyuka da musulmi suke fuskanta a cikin kasashen turai daban-daban, wanda ta bayyana hakana  amatsayin lamari mai matukar hadari, da ke bukatar hukumomin wadannan kasashe su mike haikan domin kare musulmi ‘yan tsiraru da suke rayuwa a wadanna kasashe.

 

 

4073685

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hare-hare ، cin zarafi ، wata musulma ، kasar Italiya ، jirgin kasa
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
عيسى بن عبدالله
0
0
حسبنا الله
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha