Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Wafd ya bayar da rahoton cewa, a kwanakin baya Ramadan Kadyrov ya wallafa wani faifan bidiyo na shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a shafin yanar gizo inda ya kawo ayoyin kur’ani a wata ganawa da ya yi da wasu shugabannin kasashen duniya.
A cikin wannan yanayi, ya rubuta cewa: "A gare mu da kuma Musulman Rasha, shugaban da ke karanta ayoyin kur'ani abin farin ciki ne na gaske da kuma abin alfahari."
Kadyrov ya ci gaba da cewa: "Mun ji dadin samun irin wannan shugaba mai kishin kasa, mai adalci da hikima."
Shugaban Chechnya ya rubuta game da karatun kur'ani mai tsarki da Putin ya yi yana mai cewa: mutumin da yake iya karanta kur’ani ya fahimci a bin da yake cewa, lalali ne zai zama mai karfin zuciya.