IQNA

Shahararrun Malamai Misarawa Makaranta Kur'ani a Masallacin Al-Hussein (AS) da ke birnin Alkahira

18:00 - August 12, 2022
Lambar Labari: 3487678
Tehran (IQNA) A ci gaba da kokarin da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta yi na fadada ilimin kur'ani, a jiya a masallacin Al-Hussein da ke birnin Alkahira an gudanar da taron karatun kur'ani mai tsarki tare da halartar fitattun mahardata na kasar Masar.
Shahararrun Malamai Misarawa Makaranta Kur'ani a Masallacin Al-Hussein (AS) da ke birnin Alkahira

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Yum Al-Savii cewa, a jiya (Alhamis) ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta shirya wani taron kur'ani a masallacin al-Hussein dake birnin Alkahira, a wani bangare na shirin da ma'aikatar ta yi na kasancewar manyan malamai a masallatan kasar tare da fadada ayyukansu. na karatun kur'ani da kuma farfado da aikin wa'azin masallaci.

Manyan malamai na kasar Masar da suka hada da: Sheikh Mahmoud Muhammad Hassan al-Kasht, Sheikh Abdul Fattah Ali Abdul Fattah al-Tarouti, Sheikh Ahmed Tamim al-Maraghi, Sheikh Abdul Latif al-Azb Wahdan, Sheikh Taha Muhammad Shaban al-Nu' mani, Sheikh Ahmed Abu Fayouz sun halarci wannan taro na Alkur'ani.

Da zaran ayyukan masallatai suka koma kamar yadda aka saba tun kafin bullar cutar korona, ma’aikatar kula da wa’azi ta Masar ta fara wani gagarumin shiri ta hanyar shirye-shirye da ayyuka da dama na tallafi, wanda babbansu shi ne sake bayyanar da masu karatun kur’ani, a cikin irin wanda masu karatu da limamai na kungiyoyi masu matsakaicin ra'ayi wadanda suke da murya mai kyau da karatu a masallatai.

A baya-bayan nan ne ma’aikatar ba da kyauta ta kasar Masar ta yanke shawarar kawo masu karatun kur’ani a masallatai domin koyar da matasa da manya ingantattun sharuddan lafuzza da karatun kur’ani domin a taimaka musu wajen tadabburin kur’ani. Har ila yau, an shirya darussa na karatu da haddar alqurani ga mata.

از سمت چپ استاد طاروطی، قاری مشهور مصری

قاریان مشهور مصری

قاریان مشهور مصری

 

4077585

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha