Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Demiur cewa, a ranar alhamis na wannan mako mai zuwa ne 17 ga watan Satumba za a bude masallaci na farko da ya dace da muhalli a birnin Sisak na kasar Croatia.
Za a gudanar da bude wannan masallaci ne a wani biki tare da halartar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da jami'an diflomasiyya. Za ta kasance cibiyar addini ta uku mafi girma ga musulmin Croatia bayan Zagreb da Rijeka.
A cewar Alam Krankic, limamin masallacin Sisak, ginin wannan masallacin ana daukarsa a matsayin wani aiki na tarihi, domin wannan tunanin ya samo asali ne tun fiye da shekaru 50 da suka gabata, kuma ya kasance mafarkin al'ummar musulmi da dama. Ana sa ran wannan cibiya za ta yi hidima ga musulmi fiye da 4,000 da ke zaune a wannan birni.
Sabuwar cibiyar Musulunci za ta kasance a fili mai girman murabba'in mita 2,600
Daya daga cikin abubuwan da masallacin Sisak ke da shi shi ne karfin makamashin da yake da shi, don haka ne ake masa lakabi da masallaci na farko da ya dace da muhalli a wannan yanki na Turai.
Cibiyar tana da famfunan zafi, hasken rana a kan rufin da tashar wutar lantarki na tsawon kilowatt 30 da hasken wuta na LED.