Cincirindon masu zanga-zangar dai sun yi ta rera taken yin Allah wadai da kulla alaka tsakanin Masarautar Morocco da gwamnatin yahudawa, kamar yadda suka yi ta la’antar jakadan Isra'ila a Morocco, David Govrin, da ministan harkokin wajen Moroko Nasser Bourita.
Wata majiyar Isra'ila ta tabbatarwa AFP cewa, an gayyaci Govrin ne domin gudanar da bincike, wanda majiyar ba ta fayyace yanayinsa ba.
A cewar kafofin yada labaran Isra'ila, Govrin na fuskantar tuhuma kan cin zarafin mata a Morocco, da wasu tuhumce-tuhumce kan almubazzaranci da ake zarginsa da aikatawa, musamman bacewar wata kyauta da Sarkin Maroko ya aike da ita a bikin zagayowar ranar kafuwar gwamnatin yahudawan Isra'ila a yankin Falastinu da yahudawa suka mamaye, kuma Govrin bai mika kyautar ga gwamnatin Isra’ila ba.
Govrin, mai shekaru 59, ya kasance jakada Isra’ila a Masar daga shekarar 2016 zuwa Agusta 2019, kuma an nada shi shugaban ofishin kula da hulda tsakanin Isra’ila da Morocco a farkon shekarar 2021, kafin a nada shi a matsayin jakadan Isra'ila a kasar Morocco a hukumance.
A halin yanzu Govrin yana kasar Isra'ila kuma an bude bincike akansa, a cewar wata majiyar diflomasiyya a birnin Kudus.