IQNA

An ci tarar wani mai gidan abinci dan kasar Faransa saboda zagin hijabi

17:17 - December 02, 2022
Lambar Labari: 3488267
Tehran (IQNA) Wata kotu a birnin Bayonne na kasar Faransa ta ci tarar mai wani gidan cin abinci a wannan birni Yuro 600 saboda ya hana wata mata musulma shiga wannan wuri.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, mai wannan gidan abincin ya hana wata mata lullubi shiga gidan abincin a watan Maris din da ya gabata, kuma ya yi wa abokan huldarsa sharadin cewa za su iya shiga gidan abincin ta hanyar cire mayafin.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa mai gidan abincin ya amince a lokacin da ake shari'a cewa ya aikata laifin "banbanci a kan addini".

A cewar wadannan kafafen yada labarai, dole ne mai gidan abincin ya biya tarar kudin ga uwargidan mai lullubi sannan ya kammala kwas din kare hakkin bil adama da kotu ta gindaya.

Hukuncin da kotun ta yanke ya haifar da martani daban-daban a shafukan sada zumunta. Wasu sun siffanta shi da wasa; Domin irin wannan ƙaramar tarar da hukunci na iya zama abin ƙarfafawa ga waɗanda suke da irin wannan ra'ayi.

A gefe guda kuma, kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi sun soki wannan hukuncin na kotu tare da ikirarin cewa manajan gidan abincin yana da hakkin ya hana wannan mata lullubi shiga gidan abincin.

 

4103764

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mai gidan abinci ، hijabi ، kotu ، hukunci ، lullubi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha