IQNA

An Gudanar da babban taron addini na kasa da kasa  na farko a Gambia

20:59 - December 07, 2022
Lambar Labari: 3488300
Tehran (IQNA) Kasar Gambiya ta gudanar da taron mabiya addinai karo na farko a nahiyar Afirka tare da baki daga kasashen Afirka daban-daban 54 da suka hada da shugabannin addinai da jami'an gwamnati da kuma 'yan siyasa domin tattaunawa kan zaman lafiya da juna.

Kamar yadda shafin jaridar The Point ya ruwaito, wannan taro da kungiyar hadin kan musulmi ta duniya ta shirya da sunan "Malaman Afirka da ministocin harkokin addini" an gudanar da shi ne a jiya 15 ga watan Disamba a birnin Bijilo.

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow a jawabin bude taron ya jaddada cewa, matsalolin da duniya ke fuskanta na da matukar tasiri ga addini da kuma sanya ayyukan malaman musulmi su kasance masu sarkakiya da girma.

Ya fayyace cewa: Har yanzu musulmi sun kasu kashi daban-daban, har ma suna yakar junansu kamar makiya. Duk da tsoro da kalubale, akwai dama da yawa don sauya wannan yanayin.

Shugaban kasar Gambiya ya ce: Musulmi musamman matasa da masu fada aji suna da zabi da yawa don karfafa karfinsu, daidaita ra'ayinsu da dabi'unsu, da kuma bijirewa tsarin rayuwar da ba na Musulunci ba.

 

4105267

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Gambia ، na farko ، taron addini ، bijirewa ، rayuwa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha