IQNA

Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a London

21:49 - January 19, 2023
Lambar Labari: 3488522
Tehran (IQNA) Za a fara zanga-zangar kyamar wariyar launin fata a birnin London a wata mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabesque na birnin Landan cewa, taken yaki da wariyar launin fata (#MARCHAGAINSTRACISM) na ci gaba da kasancewa cikin jerin hashtag da ake ta yadawa a shafin Twitter a kasar Birtaniya bayan da ya kara nuna damuwa kan yanayin ‘yan gudun hijira da kuma kokarin yin garambawul ga dokokin aikin ‘yan gudun hijira.

Matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na korar masu neman mafaka da kuma tura su zuwa kasar Rwanda ya haifar da cece-kuce da damuwa kan makomar mutanen da ke zuwa Ingila domin neman mafaka.

Makasudin kaddamar da wannan maudu'in shine kokarin shirya zanga-zanga a watan Fabrairu domin yin Allah wadai da yadda gwamnatin Burtaniya ke mu'amala da 'yan gudun hijira da wannan kasa.

Hare-haren wariyar launin fata a Ingila ya shafi masallatai sama da 100 a baya, kuma laifukan kyamar musulmi sun karu a kasar.

A halin da ake ciki, bayanan gwamnati a Ingila da Wales sun nuna cewa laifuffukan kiyayya da addini sun kai ko wane lokaci.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4115410

captcha