Tehran (IQNA) A ci gaba da bukukuwan fajr na juyin juya halin Musulunci, za a ji mafi kyawun karatun kur’ani na suratu fajr tare da sautin mashahuran mahardatan kur'ani na duniya.

A kashi na farko, an gabatar da karatun Ahmed Ahmed Naina, shahararren makarancin kasar Masar, na tsawon mintuna 27 ga masu sauraro.