IQNA

Shirye-shiryen Najaf na bikin  13 ga  Rajab

18:16 - February 03, 2023
Lambar Labari: 3488601
Tehran (IQNA) Dubban masu ziyara ne ke shirin gudanar da bukukuwan maulidin Imam Ali Amirul Muminin (AS) a birnin Najaf Ashraf a cikin tsauraran matakan tsaro.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahed cewa, a kowace shekara dubban masu ziyara daga kasar Iraki da sauran kasashen duniya ne ke zuwa hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf Ashraf domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa da kuma cika shekaru sama da 1400 da zuwansa Kufa.

Jami'an tsaron Iraki sun sanar da daukar tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da tsaron bikin. A bangare guda kuma an shirya jerin gwano na tarbar masu ziyara, kuma ana sa ran adadin masu ziyara  zai karu sosai a gobe Asabar a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar ranar 13 ga watan Rajab da kuma zagayowar ranar da aka haifi Imam Ali (AS).

 

4119456

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: maulidin imam ali ، tsauraran matakai ، Najaf ، masu ziyara
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha