IQNA

Sweden ta hana sabon yunkurin kona kur'ani a cikin wannan kasa

12:17 - February 09, 2023
Lambar Labari: 3488636
Tehran (IQNA) A ranar Laraba ne 'yan sandan kasar Sweden suka hana wata sabuwar zanga-zanga a babban birnin kasar Stockholm, wadda ta hada da kona kur'ani mai tsarki

A rahoton Deutsche Welle Arabi, 'yan sandan kasar Sweden sun hana gudanar da zanga-zangar saboda tasirin da zai iya yi ga tsaron kasar. Bayan zanga-zangar da aka gudanar a watan da ya gabata a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm, Rasmus Paludan daya daga cikin masu tsattsauran ra'ayi a kasar Denmark ya yi kokarin kona kur'ani mai tsarki. Bayan haka, matakin Sweden ya fuskanci babban rikici.

A karkashin tsarin tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki, gwamnatin Sweden ba ta dauki wani mataki na hana zanga-zangar ba, a sakamakon haka, a yanzu tana fuskantar cikas wajen amincewa da bukatar shiga kungiyar tsaro ta NATO, sakamakon takaddamar diflomasiyya da Turkiyya.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar cewa ba zai goyi bayan yunkurin Sweden na shiga kungiyar tsaro ta NATO ba. Kawo yanzu Ankara ta hana Sweden da Finland shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Domin sabuwar kasa ta shiga kungiyar tsaro ta NATO, dole ne dukkan kasashe mambobin kungiyar 30 su amince da karbar sabuwar mamba. Ya zuwa yanzu dai kasashe 28 ne suka amince da zama mamban kasashen Sweden da Finland, sannan kasashen Hungary da Turkiyya na adawa da shi.

Bayan tuntubar Hukumar Leken Asiri ta Sweden, hukumomin Sweden sun fayyace: zanga-zangar da aka hana ta iya kawo cikas ga tsaron kasa. Ba da dadewa ba, Norway ma ta hana kona kur'ani a wannan kasa saboda barazanar da ake yi wa tsaron kasarta.

 

 

4120910

 

captcha