IQNA

Iran Ta Yi Allawadai Da Kakkausar Murya Kan Keta Alfarmar Kur'ani A kasar Demark

21:20 - March 28, 2023
Lambar Labari: 3488882
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Iran ta yi suka da kakkausar murya kan wulakanta kur'ani mai tsarki da wata kungiya mai tsatsauran ra'ayi ta kasar Denmark ta yi a baya-bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan'ani ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, kasa da mako guda bayan kungiyar masu tsatsauran ra'ayi da kyamar musulmi da aka fi sani da Patrioterne Gar Live, ta kona kur'ani a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen.

A lokacin da yake gargadi game da karuwar cin mutuncin musulmi da ke alfarmar kur'ani mai tsarki, Kan'ani ya yi tir da shirun da wadanda ake kira masu fafutukar kare hakkin bil'adama suka yi, a yayin da suke ganin irin wadannan matakan na tozarci ga musulmi da cin zarafi ga musulmi a duk inda suke.

Haka nan kuma ya ce "Wadannan matakai ne ke share fagen nuna kyama da tsattsauran ra'ayi da kuma haifar da tashin hankali, wadanda ke haifar da hadari ga zaman lafiya a tsakanin bil'adama, da kuma tsaro.

 

4130186

 

captcha