Ayatullah Mujtahedi, yayin da yake bayani kan wani bangare na addu’ar ranar 10 ga watan Ramadan yana cewa: “Idan kana son sanin ko za a amsa addu’arka ko ba za a amsa ba, to ka koma ga zuciyarka, idan ka ga a kusurwar zuciyarka na fatan alheri wanin Allah, ka sani ba za a amsa addu’arka ba, amma idan ka yanke kauna daga komai kuma zuciyarka tana cikin kirjin Allah, ka sani cewa addu’ar ka ta karba.

A cikin watan Ramadan ne iqna ta gabatar da wata ‘yar gajeriyar addu’a ta wannan wata mai alfarma, wadda ta dace da masu azumi da kuma yada ta a shafukan sada zumunta.