A cikin faifan bidiyo guda biyu, zaku iya ganin karatun wannan matashin mai karantarwa da kuma martanin da kwamitin shari'a ya yi game da wannan aiki, wanda shine karatun ayoyi 5 na farkon suratu Fath.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Yunus Shahmoradi, wani makarancin kasar Iran ne da ya halarci gasar kur’ani ta kasa da kasa da aka gudanar a kasar Saudiyya zagaye na biyu da aka fi sani da “Atar al-Kalam” ya samu galaba a kan sauran takwarorinsa da suka fafata da su ta hanyar yin karatu mai kyau da inganci a matakin karshe na wannan gasa. ya lashe matsayi na farko a wannan gasa.
A cikin bidiyon da ke ƙasa, kuna iya ganin karatun wannan fitaccen makaranci dan kasar Iran a mataki na ƙarshe.