Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, jaridar Yediot Ahronot ta kasar Falasdinu ta bayyana cewa, mahukuntan gidan yarin sun fahimci cewa Adnan ya rasa hayyacinsa a cikin dakin da yake kadaici inda nan take aka kai shi gidan yarin Asav Herviyeh daga karshe ya sanar da shahadarsa.
Kungiyar Jihad Islami da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun sha yin gargadi game da yiwuwar shahadar wannan fursuna na Palasdinawa.
Asir Adnan dai ya shiga yajin cin abinci ne tun kwanaki 85 da suka gabata domin nuna adawa da kamun da aka yi masa ba bisa ka'ida ba, kuma duk da halin da yake ciki, kotun gwamnatin Sahayoniya ta ki sakinsa.
Kakakin kungiyar Jihad Islami Tariq Ezzeddin ya yi gargadin a jiya cewa, idan har aka samu shahadar Asir Adnan, alhakin dukkan sakamakon zai kasance kan gwamnatin sahyoniyawan.
Wannan fursunonin Bafalasdine yana daya daga cikin jagororin kungiyar Jihad Islami a yammacin gabar kogin Jordan.