IQNA

Gabatar da dokar hana kyamar Musulunci a gaban Majalisar Dokokin Amurka

15:47 - June 10, 2023
Lambar Labari: 3489284
Sanatoci uku na Amurka sun gabatar da kudirin yaki da kyamar Musulunci a duniya ga Majalisar dokokin kasar domin amincewa.
Gabatar da dokar hana kyamar Musulunci a gaban Majalisar Dokokin Amurka

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, wakilan jam’iyyar Democrat uku a majalisar dokokin Amurka sun gabatar da kudirin dokar yaki da kyamar Musulunci a duniya a karo na biyu ga majalisar dokokin kasar.

An dauki wannan matakin ne a matsayin martani ga karuwar masu kyamar Musulunci a duniya.

A cewar wata sanarwa da aka buga jiya, wakiliyar Minnesota Ilhan Omar, dan majalisar dattawan New Jersey Cory Booker da wakilin Illinois Jan Schakowsky sun sanya hannu kan kudirin.

Kudirin da aka mika wa Majalisa ya bukaci ma'aikatar harkokin wajen kasar ta nada wakili na musamman da zai sa ido da yaki da kyamar Musulunci.

Sanarwar ta kuma ce, za ta samar da cikakkiyar dabarar jagorantar Amurka wajen yaki da kyamar Musulunci a duniya. An ce 'yan majalisa 21 ne suka goyi bayan wannan kudiri.

A cikin wannan bayani, Sanata Booker ya ce: "Ayyukan da ke damun al'umma da kuma hare-haren kyamar Musulunci na ci gaba da yin barazana ga tsaro da rayuwar al'ummar musulmi a gida da ma duniya baki daya."

An ba da misali da 'yan kabilar Uygur na kasar Sin, da 'yan kabilar Rohingya a Myanmar, da kuma al'ummar musulmi a Indiya da Sri Lanka da ke fuskantar kyamar Musulunci.

A cewar wannan rahoto, masu kare ra'ayin farar fata a New Zealand da Canada su ma sun mayar da musulmi a matsayin wadanda ake kaiwa hare-haren kyamar Musulunci.

Booker da Omar sun fara gabatar da kudirin dokar kyamar Musulunci ga Majalisa a ranar 14 ga Disamba, 2021. An amince da wannan kudiri ne da kuri'u 219 masu rinjaye a majalisar wakilai; Amma Majalisar Dattawa ta ki amincewa da shi.

4146686

 

captcha