IQNA

Wani Matashi Bafalestine Ya Yi Shahada Wasu 18 Sun Jikkata A Wani Harin Isra’ila

14:19 - July 20, 2023
Lambar Labari: 3489509
Ramallah (IQNA) Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki a birnin Nablus da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan tare da kashe Bafalestine daya.

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki a birnin Nablus da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan tare da yin artabu da Falasdinawa, inda suka kashe wani matashi tare da jikkata wasu sha takwas.

Sojojin gwamnatin na yin rakiyar wasu gungun yahudawa 'yan ta'adda masu tsatsauran ra’ayi, da suka hada da sufeton 'yan sanda Kobi Shabtai da wasu jami'an 'yan sanda, wadanda suka kutsa kai a makabartar annabi Yusuf da safiyar yau Alhamis.

Ziyarar ta bakanta ran musulmi Falastinawa wanda hakan ya haifar da arangama tsakanin Falasdinawa na yankin da jami’an tsaron Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran WAFA na Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, Bader Sami Masri mai shekaru 19 da haihuwa ya hadu da ajalinsa bayan da sojojin yahudawa suka harbe shi da bindiga, inda ya samu munanan raunuka, bayan isa da shi asibiti kuma ya yi shahada.

 

4156493

 

 

captcha